IQNA

21:45 - January 15, 2022
Lambar Labari: 3486822
Tehran (IQNA) Jami'ai a jihar Illinois ta Amurka na shirin kaddamar da ranar karrama shahararren dan damben nan musulmi Muhammad Ali Kelly.

Jaridar Chicago Tribune ta bayar da rahoton cewa, a daidai lokacin da ranar Martin Luther King Jr. a Amurka, jihar Illinois ke bikin ranar tunawa da Muhammad Ali ta farko a ranar 17 ga watan Janairu a matsayin wani bangare na kudirin  amincewa da gudummawar da Amurkawa mabiya addinai daban-daban suka bayar.

Babbar jami'a a gwamnatin jihar illinois Fatemeh Siddique ta ce "Muna ganin wannan a matsayin wata dama ce ta bikin wadannan manyan gwaraza jarumai guda biyu da kuma yadda suke da alaka da juna da kuma yadda suka dace da al'adunmu na gama gari,"

Ƙungiyar Musulman Illinois Civic Alliance, ƙungiya ce ta masu fafutuka da ke jagorantar yunƙurin amincewa da ranar Muhammad Ali a duk faɗin jihar a matsayin wani ɓangare na babban kudiri da ya ƙunshi lokuta na tarihi wanda ya haɗa da nazarin gudunmawar Amurkawa mabiya addinai daban-daban.

Domin yada labarai game da ranar farko ta Mohammad Ali, an buga hotuna daban-daban na Muihammad da kowa zai iya nema kyauta ta hanyar amfani da fom na Google a yanar gizo.

 

4028500

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mabiya addinai ، daban-daban ، kyauta ، babban kudiri ، masu fafutuka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: