IQNA

18:38 - January 16, 2022
Lambar Labari: 3486826
Tehran (IQNA) Majiyoyin tsaro a kasar Iraki sun sanar da kaddamar da wani gagarumin farmaki a yankin Tarmiyah da ke arewacin Bagadaza, da nufin lalubo wasu mayakan kungiyar Daesh da suka samu maboya a wuraren.

Majiyoyin tsaron suka ce, runduna ta 12 ta Al-Shabaab ta kaddamar da wani gagarumin aikin tsaro domin bincike da kuma duba yankin Tarmiya da ke arewacin Bagadaza, da kuam tsarkake yankin daga ‘yan ta’addan da kuma barazanar tsaro.

A cewar wadannan majiyoyin, wannan farmakin na jami’an tsaro na da nufin nemo boyayyun gungun ‘yan ta’adda na ISIL a yankin da kuma fadada tsaron al’ummar wannan yanki.

Manjo Janar Mahmoud al-Fallahi, kwamandan ayyukan tsaro na musamman a lardin Ninawa, yayin da yake jaddada yaki da kungiyar ta'addanci ta Da'ish, ya yaba da muhimmiyar rawar da manyan gwaraza suka bayar wajen karya lagon ‘yan ta’addan daesh, musamman manyan kwamnadoji da suka hada da Qassem Sulaimani da Abu mahdi Al muhandis, wadanda suka kafa rundunar Hashd Al-shaabi.

Al-Fallahi ya ce: “A yau garuruwanmu suna cikin aminci saboda sadaukarwar da wadannan manyan shahidai suka yi

Ya kara da cewa: An samu nasarar a kan ISIL ne da kokarin jami'an tsaro da Hashd al-Shaabi.

A dai dai lokacin da ake ci gaba da tada jijiyoyin wuya ta fuskar siyasa ne a kasar ta Irakin na jaddada bukatar janyewar sojojin Amurka daga kasar, ayyukan kungiyar ta'addanci ta Da'esh ke kara zafafa.

4028831

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: jaddada ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: