IQNA

Wata Baturiya Da Ta Musulunta A Burtaniya Ta Zabi Sunan Fatima

21:44 - January 25, 2022
Lambar Labari: 3486867
Tehran (IQNA) Gabriela Wata yarinya ce ‘yar kasar Birtaniya ‘yar shekaru 22 da ta musulunta ta bayyana hakan ne a wani biki da aka gudanar a cibiyar Musulunci ta Birtaniya da ke birnin Landan.

Wata yarinya ‘yar kasar Birtaniya mai suna Gabriela ‘yar shekaru 22 da ta musulunta ta bayyana hakan ne a wani bikin maulidin Fatima Zahra (AS) da aka gudanar a cibiyar Musulunci ta Birtaniya da ke birnin Landan, inda ta ce tana alfahari da samun sunan Musulunci da ake kira Fatima daga yanzu.

Maulidin diyar manzon Allah S.A.W a cibiyar musulunci ta kasar Ingila a bana ba a taba yin irinsa ba idan aka kwatanta da shekaru ashirin da suka gabata, yayin da daruruwan mabiya mazhabar ahlul bait dake zaune a birnin London na kasar daga kasashe daban-daban , Labanon, Iraki, Afirka, Afganistan, Bahrain, Siriya da Saudiyya sun halarci bukin karrama Sayyida Zahra (AS) a taro mara misaltuwa. 

A cewar Cibiyar Musulunci ta Ingila; Hojjatul Islam Seyyed Hashem Mousavi, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran a kasar Burtaniya, a wani jawabi da ya yi cikin harsunan Ingilishi da Farisa, yayin da yake ishara da fadar Ubangiji kan kyautatawa da jin kai ga iyaye, ya ce: “Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana matsayi da hakkokinsu a matsayin wajibi a kan dukkanin masu imani.

4031350

 

 

 

captcha