IQNA

Za A Yi Bikin Karrama 'Yan Wasa Masu Adawa Da Zaluncin Isra'ila

22:07 - January 29, 2022
Lambar Labari: 3486882
Tehran (IQNA) kungiyar da ke fafutukar kamfe mai taken komawa Palastinu (GCRP) ta sanar da cewa za ta shirya gudanar da taron kasa da kasa don karrama 'yan wasan da ke adawa da daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan a Beirut, babban birnin kasar Labanon.

Tashar Falastine Yaum ta bayar da rahoton cewa, kungiyar da ke jagorantar Kamfe na duniya  mai taken komawa Falasdinu, ta sanar da gudanar da wannan taro kwanaki kadan da suka gabata ta hanyar wallafa wani sako a shafinsa na Twitter.

Taron wanda ake kira "Kasar Zinare ta Qudus" zai fara gudana ne a ranar 31 ga watan Janairu mai kamawahar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu mai kamawa, inda za a karrama 'yan wasan da ke adawa da daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan.

Kungiyar ta bayyana a shafinta na twitter cewa: A cikin wannan dandalin an yabawa jaruman 'yan wasa saboda kin fuskantar 'yan wasan gwamnatin Isra'ila a gasar wasanni na kasa da kasa saboda adawa da daidaita alaka da makiya al'ummar musuulmi da larabawa.

Gangamin Komawa zuwa Falasdinu ƙungiya ce daga cikin ƙungiyoyi masu zaman kansu wadda take da ammbobi daga ƙasashe 80 na duniya.

A cewar masu fafutuka, an kafa dandalin ne domin tallafawa 'yancin 'yan gudun hijira Falastinawa domin komawa kasarsu Falasdinu da yahudawa suka haramta musu.

 

https://iqna.ir/fa/news/4032252

 

captcha