IQNA

Tarayyar Afirka Ta Jingine Matsayin Da Ta Baiwa Isra'ila Na Mamba Mai Sanya Ido A Kungiyar

17:19 - February 06, 2022
Lambar Labari: 3486914
Tehran (IQNA) Taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka da ke gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya dakatar da matakin bai wa Isra'ila matsayin mamba 'yar kallo a kungiyar.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Matakin da babban taron kolin shugabannin kasashen Afirka ya amince da shi a yau, ya hada da dakatar da kudirin Moussa Faki babban kwamishinan zartawa na kungiyar, kan baiwa Isra'ila matsayin mamba 'yar  kallo a kungiyar ta AU a ranar 22 ga watan Yuli, da kuma kafa kwamitin da ya kunshi shugabannin kasashen Afirka 7 da za su ba da Shawarwari ga taron kolin AU.

Kwamitin ya hada da Shugaba Macky Sall na Senegal a matsayinsa na shugaban kungiyar Tarayyar Afirka na yanzu, shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune, shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Felix Tshisekedi, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Buhari da shugaban Kamaru Paul Biya.

Tun bayan da babban kwamishinan zartawa na kungiyar tarayyar Afirka Musa Faki ya bayar da kujerar mamba 'yar kallo ga Isra'ila a cikingiyar tarayyar Afirka, kasashe da dama a cikin kungiyar suka nuna rashin gamsuwarsu da hakan, lamarin da ya jawo rarrabuwar kawuna tsakanin mambobin kungiyar.

A zaman na yau dai dukkanin kasashe mambobin kungiyar tarayayr Afirka ne suka amince da a dakatar da matakin baiwa Isra'ila wanann kujera, har sai an samu shawarwarin kwamitin da aka kafa kan hakan.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4034317

captcha