IQNA

Baje Kolin Hijabin Musulunci A Kasar Tanzania

22:28 - February 06, 2022
Lambar Labari: 3486917
Tehran (IQNA) Mai ba da shawara kan al'adu na kasar Iran tare da hadin gwiwar cibiyar Pink Hijabi da ke Tanzaniya ne suka gudanar da bikin baje kolin Hijabi na duniya.

A yayin bikin ranar hijabi ta duniya tare da taimakon mai ba da shawara kan harkokin al'adu na kasar Iran a Tanzaniya da hadin gwiwar cibiyar kula da al'adun gargajiya ta kasar Tanzania, an bude bikin baje kolin Hijabi a ofishin  mai ba da shawara kan al'adun kasar Iran..

Bikin ya samu halartar shugabar ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, jakadan Indonesia, jakadan Turkiyya, mai kula da harkokin Oman a Tanzaniya, Madam Shamim Khan, shugabar sashin mata ta kasar Sin, Majalisar musulmin Tanzaniya da wasu Iraniyawa da mata masu fafutuka da dama.

Babban bako na musamman a bikin shine ministan kwadago, tattalin arziki da zuba jari na Zanzibar Roderick Ramadan Suraga.

Madam Khadijeh Omari, shugabar cibiyar Pink Hijab ta yi bayani game da irin ayyukan da cibiyar ke yi na karfafa matsayin mata a cikin al’umma.

Ms. Francesca Lee Moo, shugabar kasuwancin Pink hijab, Shamim Khan, shugabar mata na majalisar musulmin Tanzaniya, Arshadi da Mozaffari, mambobin tawagar kungiyar al'adun muslunci da sadarwa don halartar wannan baje kolin.

 

https://iqna.ir/fa/news/4034114

Abubuwan Da Ya Shafa: sadarwa
captcha