IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Da Hamas sun Yi Yaba Da Jingine Baiwa Isra'ila Izinin Zama Mamba 'Yar Kallo A Tarayyar Afirka

21:25 - February 07, 2022
Lambar Labari: 3486920
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen larabawa ta fitar da bayanin yin maraba da matakin da kungiyar tarayyar Afirka ta dauka na jingine batun baiwa Isra'ila kujerar a matsayin mamba mai sanya idoa kungiyar.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, kungiyar kasashen larabawa ta fitar da bayanin yin maraba da matakin da kungiyar tarayyar Afirka ta dauka na jingine batun baiwa Isra'ila kujerar a matsayin mamba mai sanya idoa kungiyar ta AU.

Ita ma kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana jin dadinta game da matakin kungiyar tarayyar Afrika na jingine maganar baiwa Isra’ila kujerar ‘yan kallo a kungiyar.

Hamas, ta yi kira ga kungiyar ta AU, da ta yi aiki da dokokin da suka shafa yaunin da ya rataya a wuyanta na yaki da mamaya da nuna wariyar laujin fata da kuma kare hakkin falasdinawa.

Kasashe da dama ne dai na Afrika suke adawa da matakin da shugaban kwamitin kungiyar Musa Faki Mahamat ya gabatar na baiwa Isra’ila kujerar ‘yar kallo a kungiyar.

Aljeriya da Afrika ta Kudu, na daga cikin kasashen da suka amincewa da batun.

Majiyoyi da dama sun ce an dakatar da tattauna batun ne yayin taron koli na 35 don kada a haifar da rudani ko rashin jituwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

 

4034360

 

captcha