IQNA

17:46 - March 01, 2022
Lambar Labari: 3486998
Tehran (IQNA) A cikin jawabin da ya yi kai tsaye da kuma ta gidan talabijin Ayatullah Khamenei ya ce: Aiko manzon Allah (SAW) wata baiwa ce ga dukkan bil'adama.

Abubuwan da ke cikin sun kunshi cewa:
Aiko Manzon Allah (SAW) wata baiwa ce ga dukkan bil'adama. Daga cikin dabi'u masu yawa na Musulunci , idan muka yi la'akari da dabi'u guda biyu kawai, wato bangaren yada hankali da tarbiyyantar da kyawawan dabi'u, za mu yarda cewa Musulunci ya ba da babbar kyauta da gudunmawa ga rayuwar bil'adama.
Musulunci ya yi kira zuwa ga yin aiki da hankali da fadada hankali, wanda yake da muhimmanci.
Dangane da ci gaban akidu da tarbiyyar kyawawan halaye, ya isa Musulunci ya ambaci manufofin kyawawan halaye da tsarkake ruhi a cikin rayuwar mutum, inda Alkur'ani ya ambaci tsarkake rai a matsayin makasudin wahayi.
Wani abu game da aiko manzo shi ne cewa, manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya samu wani abu da ake ganin ba zai taba yiwuwa ba; shi ne canja dabi’a  ta al’ummar yankin Larabawa a zamanin jahiliyya, da kafa al’umma tagari irin al’ummar musulmi a wancan zamani.
Lokacin da aka sanya nufin daidaikun mutane bisa nufin Ubangiji, kuma aka karkata zuwa ga nufin Ubangiji, ’yan Adam na iya yin abubuwan da suke ganin ba za su taba yiwuwa ba, kuma za su iya cimma burin da ake ganin kamar na al’ada ne kuma ba za su iya isa gare su ba.
 
Ƙarshen yunkurin annabta shi ne kafa tsari na tafiyarwa bisa koyarwa ta addinin ubangiji.
Daya daga cikin muhimman ayyukan da Manzon Allah (SAW) ya yi a cikin wannan gagarumin aiki shi ne tinkarar jahilci. An sha yin Allah wadai da jahilci a cikin Alkur'ani.
Jahilci ba yana nufin jahilci ne kawai da jahilci da aka fi sani da rashin ilimi kan wani abu ba,. Wannan jahilci yana da ma’ana mai fadi; munanan dabi’u kansu shima wani bangare ne na wannan jahilci. Halayen dabbanci na mutane suna daga cikin jahilci daya.
Yawancin munanan dabi'un da suka yi yawa a Makka da Larabawa a wancan lokacin sun wanzu har zuwa  yau a cikin abin da ake kira duniyar Yammacin Turai a cikin dabi’unsu.
Dangane da yakin Ukraine kuwa cewa ya yi, Muna adawa da yaki a ko’ina a duniya; Muna adawa da kashe-kashen jama’a da lalata ababen more rayuwa na jama’a.
Ba mu zama kamar mutanen yamma ba, lokacin da aka jefa bam a kan ayarin bikin aure a Afganistan, inda suke ɗaukarsa a matsayin yaƙi da ta’addanci, amma muna adawa da yaƙi a duk faɗin duniya.
A Ukraine, muna goyon bayan kawo karshen yakin. Tushen rikicin Ukraine shine a siyasar Amurka. Amurka ce ta kai Ukraine zuwa wannan matsayi, kuma ita ummul haba’isin haddasa wannan rikici.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4039625

Abubuwan Da Ya Shafa: Ayatullah Khamenei ، Aiko manzon Allah (SAW)
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: