IQNA

Ayyukan Da'irar Kur'ani A Haramin Makka Bayan Janye Ka'idojin Korona

15:44 - March 17, 2022
Lambar Labari: 3487063
Tehran (IQNA) An ci gaba da gudanar da ayyukan da'irar haddar kur'ani da karantarwa a masallacin Harami na Makkah bayan cire takunkumin da aka sanya saboda korona.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na "alkhaleej365.com" ya bayar da rahoton cewa, sashen kula da harkokin kur’ani mai alaka da babban daraktan masallacin harami da kuma masallacin manzon Allah (SAW) ya sanar da cewa: Bayan dage takunkumin da aka sanya saboda corona, da'irori 5 na koyar da haddar kur’ani  da tilawa a  masallacin Harami sun ci gaba da gudanar da ayyukansu.

"Badr al-Mohammadi", daraktan sashen kula da da'irar kur'ani na masallacin Harami, ya ce dangane da haka: za a gudanar da wadannan da'irar koyarwar kur'ani da yamma.

Ya kara da cewa: Bayan soke matakan kariya da aka dauka na tunkarar yaduwar korona, ana samun karuwar da'irar karantar da kur'ani a masallacin Harami.

Badar al-Mohammadi, yayin da yake ishara da yadda ake ci gaba da samun karuwar masu ziyara a wadannan da'irori na kur'ani, ya ce: "Har yanzu wajibi ne a kiyaye matakan kariya da sanya abin rufe fuska domin halartar wadannan tarukan na kur'ani.

 

https://iqna.ir/fa/news/4043818

Abubuwan Da Ya Shafa: haramin makka
captcha