A karon farko cikin kusan shekaru biyu tun daga ranar Juma’a, Musulmi a masallatai a fadin kasar Singapore ba sa bukatar yin tazara a lokacin sallar jam’i, kamar yadda jaridar Street Times ta ruwaito.
Yayin da ake yin dubi kan yanayin Covid-19 a Singapore, an rage takunkumi don ba wa masu ibada damar yin sallar Juma'a tare.
An rage matakan don ayyukan addini a ranar Talata, amma sanya abin rufe fuska yana da mahimmanci.
An kuma dage dokar hana taruwar fiye da mutum 1,000 domin gudanar da ayyukan ibada, inda a yanzu za a iya cika rabin wuraren muddun mutanen sun yi allurar rigakafi.
Majalisar Musulunci ta kasar Singapore (Muis) ta bayyana cewa masallatai za su bude wasu wurare kuma za su bayyana karin bayani nan da makonni masu zuwa.