A rahoton da kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar an bayyana cewa, jami'an Taliban sun ce an kai wani harin bam a yammacin yau Litinin a Mazar-e-Sharif, babban birnin lardin Balkh.
Kungiyar Taliban dai ba ta bayar da wani bayani kan hasarar rayuka ba, amma shaidun gani da ido sun ce an kashe mutum daya tare da jikkata wasu da dama.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka kai harin a lardin Balkh tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe iko da Afganistan, kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.