IQNA

Yau ake fara I'itikafi na Ramadan a masallacin Annabi (SAW)

15:48 - April 21, 2022
Lambar Labari: 3487197
Tehran (IQNA) Mutanen da ya kamata su shiga ibadar I’itikafi a masallacin Annabi da ke Madina za su shiga wannan masallaci daga yau.

Kamar yadda jaridar Arab News ta ruwaito, adadin wadannan mutane dubu hudu ne kuma tuni suka yi rajistar yin ibadar I’itikafi a masallacin Annabi.

Ana yin I’itikafi ne a kwanaki 10 na karshe na watan Ramadan, a lokacin da masu ibada ke kadaita da yin addu’a da karatun Alkur’ani.

Ana fara I’itikafi a Masallacin Nabi da yammacin ranar ashirin ga watan Ramadan, sannan kuma a kammala da ganin watan Shawwal da kuma farkon Sallar Idi. A lokacin i’itikafi, masu ibada suna zaune suna kwana a cikin masallatai.

A cewar jami’an masallacin, a lokacin buda baki da sahar, ana samar da abubuwan sha masu zafi da sanyi da kuma aikin share wurin da tsaftace shi, domin jin dadin mahajjata a masallacin Annabi. Za a kuma sami damar yin wa'azin addini a cikin harsuna da dama.

Tun da farko, Babban Darakta na Wurare masu Tsarki ya ba da izinin yin  ibadar I’itikafi a wannan shekara.

An dakatar da ibdar ne shekaru biyu da suka gabata saboda yaduwar cutar korona, amma ana raba abincin buda baki da aka shirya ga mahajjata.

Duk da saukaka dokar hana fita da aka yi a Saudiyya, jami'ai sun bukaci masu ibada da su kiyaye ka'idojin kiwon lafiya.

 

https://iqna.ir/fa/news/4051429

captcha