IQNA

A Ranar Quds Ta Duniya Yahudawa Sun Aukawa Musulmi A Cikin Masallacin Quds

17:15 - April 29, 2022
Lambar Labari: 3487230
Tehran (IQNA) Dakarun gwamnatin sahyoniyawan sun kai hari a safiyar yau 29 ga watan Afirilu a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan ranar Qudus a masallacin Al-Aqsa inda suka yi arangama da Falasdinawa masu ibada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton jaridar Quds Al-Arabi, a yayin farmakin sojojin gwamnatin mamaya sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi a kan Palasdinawa, sannan kuma matasan Palasdinawa sun yi ta jifa da duwatsu domin kare kansu.

‘Yan sandan yahudawan sahyuniya sun kuma hana matasa masu ibada shiga masallacin, kuma shaidun gani da ido sun ce an jikkata wasu Falasdinawa a wurin.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bayar da rahoton cewa, Falasdinawa 12 ne suka jikkata a rikicin masallacin Al-Aqsa kuma an ba su agajin gaggawa sannan aka kai su asibitin Al-Maqassid.

Tun a ranar Juma'ar da ta gabata daruruwan Falasdinawa ne suke gudanar da addu'o'i a masallacin Al-Aqsa, kuma a safiyar yau daruruwan Falasdinawa ne suka shiga masallacin Al-Aqsa suna kabbara domin gudanar  da sallar Juma'a a masallacin a ranar Juma'ar karshe ta watan Ramadan, lokacin da 'yan mamaya suka kai musu hari.

4053432

 

 

captcha