IQNA

Yau ce ranar farko da ake fara duba watan Shawwal a Najeriya

16:34 - April 30, 2022
Lambar Labari: 3487235
Tehran (IQNA) Majalisar koli ta al-amuran musulmi a tarayyar Najeriya ta bukaci musulman kasar su fara neman ganin jinjirin watan Shawwal a yammacin yau Asabar.

Labarin ya kara da cewa Malam Zubair Haruna shugaban bangaren zartarwa na majalisar ne ya bayyana haka a wani rahoton da ya fitar a madadin shugaban majalisar Sultan Sokoto.

Labarin ya kara da cewa idan ba’a sami damar ganin watan a yau 30 ga watan Afrilu ba, za’a cika watan ramadan 30 ta yadda ranar Litinin zata kasance daya ga watan shawwal na wannan shekara ta 1443.

Idan kuma an ga wata daga wajen mutane adilai, shugaban majalisar zai bada sanarwa kan gobe lahadi ta zama ranar daya ga watan shawwal kuma ranar Sallah karama.

 

4053707

 

 

captcha