IQNA

Tsohon dan wasan kwallon kafar Kamaru ya Musulunta

16:45 - May 14, 2022
Lambar Labari: 3487291
Tehran (IQNA) Tsohon dan kwallon Kamaru Patrick Ambuma ya Musulunta a wani masallaci da ke daya daga cikin garuruwan kasar. Ya zabi sunan Musulunci "Abdul Jalil".

Kamar yadda jaridar Egypt Times ta ruwaito, Patrick Ambuma, fitaccen dan wasan kwallon kafar Kamaru, ya bayyana a jiya cewa ya musulunta a gaban dimbin jama’a a wani masallaci da ke birnin Douala a ranar Juma’a 13 ga watan Mayu.

Kafofin yada labarai sun watsa wani faifan bidiyo da ke nuna Ambuma sanye da rigar Musulunci, inda ya bayyana cewa ya Musulunta, ya kuma canza sunansa zuwa Abdul Jalil.

An haifi Patrick Ambuma a shekara ta 1970 a Douala. Ya buga wa tawagar kwallon kafar Kamaru daga shekarar 1995 zuwa 2002, inda ya buga wasanni 56 ya kuma ci kwallaye 33.

Ambuma ya taka leda a gasar cin kofin duniya a shekarun 1998 da 2002, inda ya lashe gasar cin kofin Afrika da tawagar kasar Kamaru a shekarar 2000 da 2002, ya kuma lashe zinare a gasar Olympics ta Sydney a shekara ta 2000.

Ya taka rawar gani sosai a lokacin da yake taka leda, inda ya zura kwallaye a gasar cin kofin Afrika guda uku a shekarar 2000 a Ghana da Najeriya, a shekarar 2002 a Mali da kuma a shekarar 2004 a Tunisia tare da zakarun Kamaru.

Ana yi masa kallon daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa a tarihin ‘yan wasan kasar Kamaru kuma yana cikin jerin ‘yan wasan da suka fi zura kwallo a raga a tarihin gasar cin kofin Afrika da kwallaye 11.

Ambuma ya kuma taka leda a kungiyoyi da dama da suka hada da Paris Saint-Germain da Chateauroux a Faransa da Gamba Ozakia na Japan da Cagliari a Italiya da Ittihad Libya da Tokyo Verdi na Japan.

ستاره سابق تیم ملی فوتبال کامرون به اسلام گروید + فیلم

 

https://iqna.ir/fa/news/4056905

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :