IQNA

Surorin Kur’ani   (7)

Surar A'araf; Siffar rashin cika alkawalin mutum ga Allah

17:54 - May 31, 2022
Lambar Labari: 3487367
An bayyana ra'ayoyi da mahanga daban-daban game da halittar mutum da halittu, amma a mahangar Musulunci, Allah ya halicci duniya baki daya da 'yan Adam a cikin wani lokaci; Kamar yadda addinin musulunci ya tanada, ’yan Adam sun yi alkawari da Ubangijinsu kafin yin halitta domin su zama magajin Allah a duniya.

Sura ta bakwai a cikin Alkur’ani mai girma ana kiranta da suna “A’araf” wacce ke dauke da ayoyi 206 a cikin sashe na takwas da na tara na Alkur’ani; Saukar Suratul A'araf ta sauka ne ga Annabi a cikin mafi tsananin yanayi na musulmi, wato a lokacin da aka yi wa tattalin arzikin Makka kawanya.

Suratul A’araf kamar sauran surorin Makkah, ta yi bayani ne akan mas’alolin halitta, da hujjar tauhidi, da gwagwarmaya da shirka, da bayyana matsayin mutum a duniyar halitta. Kuma tun da aka siffanta farkon halitta, yana tunatar da mutum alƙawuran da ya yi da Allah tun farkon halitta; Haka nan don nuna sakamakon kaucewa tafarkin tauhidi, ya yi bayani ne kan tarihin qabilu da annabawa da suka gabata kamar Nuhu (AS) da Ludu (AS) da Shoaib (AS).

Ana iya lissafta manyan batutuwan suratu A'araf kamar haka;

halittar mutum

Wannan sura ta yi magana dalla-dalla game da halittar Adamu da Hauwa’u, mutane biyu na farko, yaudararsu daga shaidan da fita daga aljanna, da yadda suka fara rayuwa a duniya.

Anas da Alqur'ani

Ya ambaci Alkur’ani mai girma a matsayin littafi na Ubangiji bisa tafarkin shiriya da rahamar Ubangiji na musamman ga talikai, kuma ya kira ranar kiyama ranar tafsirin Alkur’ani.

Farkon halittar kasa da sama

Haka nan kuma, ta yi bayanin farkon halittar sammai da kassai, kuma tana siffanta shiriya da batar da mutane dangane da Ubangijinsu.

Labarin Annabi Musa (AS)

Kuma an yi bayanin kissar Annabi Musa (AS) dalla-dalla a cikin wannan sura. Da farko tana magana ne akan abubuwan da suka faru tsakanin su da Fir’auna, sannan kuma ta bayyana “halayen bani Isra’ila” da Musa (AS).

Alkawuran Allah

Haka nan kuma ana tunawa da alkawuran da aka yi tsakanin mutum da Allah da kuma dora mutum alhakin shirka da imaninsa, kuma dangane da haka, ana ba da labari kan kokarin annabawa na shiryar da mutane.

Lahira

Batun tashin kiyama kuma wani lamari ne da aka ambata a cikin wannan sura; Al'amarin da babu wanda ya sani sai Allah.

Labarai Masu Dangantaka
Abubuwan Da Ya Shafa: annabawa shiryar da mutane alhakin
captcha