IQNA

An saka kyallen dakin Ka’aba mai alfarma

16:10 - June 20, 2022
Lambar Labari: 3487445
Tehran (IQNA) an fara shirye-shiryen fara aikin hajjin bana, inda a jiya aka saka kyallen dakin Ka’abah.

A cewar Al-Madina, masu kula da Masallacin Harami bisa al'adar kowace shekara da jajibirin lokacin Hajji na shekarar 1443, bayan an yi sallar Magriba a daren jiya, sai suka daga labulen dakin Ka'aba da mita uku, sannan suka sanya farin kyalle mai fadin mita 2 a kusa da shi.

Babban Darakta na Al-Masjid Al-Haram ya sanar da cewa, 'yan sa'o'i kadan bayan Magriba a yammacin Lahadi an sanya wani farin kyalle na  auduga a dukkan bangarori hudu na dakin Ka'aba yayin da mahajjata ke gudanar da ibada da dawafi a Dakin Allah.

Da wannan ibada, yayin da ake saka labulen dakin Ka’aba, an lullube shi da ihrami kuma an lullube shi da fararen kyallaye , ta haka ne ake shirya kwanakin aikin Hajji, wanda zai fara a kasa da kwana 20 masu zuwa.

4065334

 

Abubuwan Da Ya Shafa: lullube ، kyalle ، ibada ، Magriba ، dakin Ka’aba
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha