IQNA

Sanya kyamarori sama da dubu a Karbala don tabbatar da tsaron maziyarta

17:34 - July 15, 2022
Lambar Labari: 3487550
Tehran (IQNA) A jajibirin watan Muharram rundunar ‘yan sandan Karbala ta sanar da kafa karin kyamarori sama da 1000 a kofofin shiga da fita na Karbala da ciki da kuma kewayen wuraren ibada na alfarma domin tabbatar da tsaron mahajjata.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-Sumaria cewa, hukumar ‘yan sanda ta Karbala ta sanar da cewa, a cikin tsare-tsaren tsaro a lardin na Karbala, an gudanar da aikin sanya na’urorin daukar hoto sama da dubu a dukkanin mashigin shiga da fita na lardin na Karbala da yankuna daban-daban na birnin. ciki da kewayen Wuri Mai Tsarki.ya gama

نصب بیش از 1000 دوربین هوشمند در کربلا برای تامین امنیت زائران عتبات عالیات/اماده

A cikin wata sanarwa da ta fitar, wannan cibiya ta jaddada cewa: Domin karfafa tsaro a lardin da kuma gano mutane da dama da jami'an tsaro ke nema ruwa a jallo, da kuma samar da karin tsaro ga mahajjata a Karbala, 'yan sandan wannan lardin sun sanya na'urorin daukar hoto na zamani.

نصب بیش از 1000 دوربین هوشمند در کربلا برای تامین امنیت زائران عتبات عالیات/اماده

A cewar wannan sanarwar, yayin da ake saka sabbin na’urorin daukar hoto, an gano wasu da dama da ake nema ruwa a jallo, tare da kame wasu da dama da ake nema ruwa a jallo, kuma an kara samun zaman lafiya a lardin.

4070964

 

captcha