IQNA

An Rarraba Cake mafi girma a duniya a hubbar Imam Ali (AS)

14:41 - July 19, 2022
Lambar Labari: 3487564
Tehran (IQNA) A ranar litinin 18 ga watan yuli ne ake gudanar da zagayowar ranar Allah Ghadir masoya sayyidina Amirul Muminin Ali (AS) suka yi wa alhazan Shah Najaf dadi ta hanyar yin cake mafi girma a duniya.

Kamar yadda Iqna ta ruwaito; Masoyan Sayyidina Amirul Muminin Ali (AS) sun yi wa alhazan Shah Najaf dadi, ta hanyar gasa cake mafi girma a duniya domin girmama ranar Ghadir.

Wannan cake da masoya Imam Ali (AS) da Ahlul Baiti (AS) na Iran suka gasa, an kawata shi tare da raba shi ga maziyarta.

Wannan babban cake ya kai ton 200 kuma an raba shi ne ga masu ziyara a hubbaren Imam Ali (a.s.) tare da hadin gwiwar cibiyar kula da hubbaren.

Tsawon wannan cake  ya kai mita 1433, wanda shi ne irinsa na farko da aka taba yi a duniya.

 
 

 

4071734

 

Abubuwan Da Ya Shafa: rarraba zagayowar ahlul bait imam ali kawata
captcha