IQNA

14:37 - October 24, 2022
Lambar Labari: 3488061

Mauritania; Nouakchott  Babban birnin al'adun Musulunci a 2023

Tehran (IQNA) Ministan al'adu na Mauritania ya sanar da fara shirye-shiryen gabatar da Nouakchott a matsayin babban birnin al'adun Musulunci a shekarar 2023.

Mauritania; Nouakchott  Babban birnin al'adun Musulunci a 2023

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sahra Media cewa, ministan al'adun kasar Mauritaniya Mohamed Oulad Aswaidat ya bayyana cewa: Wannan ma'aikatar ta fara shirye-shirye a aikace domin Nouakchott ta zama hedikwatar al'adun muslunci a shekarar 2023.

Ministan al'adu na kasar Mauritania ya bukaci kasashe mambobin kungiyar ISESCO da su taimaka wajen tsara ayyukan wannan taron.

Da yake jawabi a wajen taron ministocin yada labarai na kungiyar kasashen musulmi da aka gudanar a kasar Turkiyya, ya bayyana cewa, an zabi Nouakchott a matsayin hedkwatar al'adun muslunci a shekarar 2023 bisa kudurin kungiyar raya ilimi da al'adu da kimiyya ta Musulunci ta ISESCO.

4093947

 

 

captcha