IQNA

Yajin cin abinci na fursunonin Falasdinu a watan Ramadan

14:45 - March 12, 2023
Lambar Labari: 3488796
Tehran (IQNA) Fursunonin Falasdinawan da ke gidajen yarin gwamnatin sahyoniyawa na shirye-shiryen yajin cin abinci a watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misri Alyoum cewa, fursunonin Palastinawa a matsayin mayar da martani ga tsauraran matakai da gwamnatin sahyoniyawan ta ke shirin yi musu, suna ci gaba da nuna rashin amincewarsu ga hukumomin gidajen yari na gwamnatin a rana ta 26 a jere.

A cewar sanarwar da hukumar kula da fursunoni da kuma kungiyar ‘yan fursunoni ta Falasdinu ta fitar, za a ci gaba da wannan bijirewa har sai an fara yajin cin abinci na fursunoni a farkon watan Ramadan.

Yajin cin abinci na fursunonin Palasdinawa ya yi daidai da shirin da kwamitin kolin kula da harkokin fursunonin Falasdinu ya yi, inda dukkanin kungiyoyin Falasdinu ke da wakilci.

Fursunonin Palastinawa sun fara ayyukansu ne a matsayin mayar da martani ga ayyukan yahudawan sahyuniya tun a ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata da kuma bayan sanar da fara aiwatar da matakan da Itmar Ben Guer ministan tsaron cikin gidan gwamnatin sahyoniyawan ya yi niyya ga fursunonin Palasdinawa.

 

4127492

 

captcha