IQNA

Za A Fassara jawabin jagora a lokaci guda a cikin harsuna karkashin wani tsari na hubbaren Radhawi

15:39 - March 18, 2023
Lambar Labari: 3488827
Tehran (IQNA) Daraktan kula da harkokin ziyara na hubbaren Imam Ridha (AS) na wadanda ba Iraniyawa ba ya ce: Za a fassara jawabin Nowruz na Jagoran juyin juya halin Musulunci a ranar farko ta sabuwar shekara zuwa harsunan Ingilishi da Larabci da Azeri da kuma Urdu a Haramin.

Hojjat-ul-Islam wal-Muslimeen Sayyid Mohammad Zulfiqari, manajan bangaren kula da ayyukan  maziyarta  wadanda ba Iraniyawa ba, a wata hira da ya yi da IQNA ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci zai gabatar da jawabi a ranar farko ta sabuwar shekarar shamsiyya, ga masu ziyara a hubbaren Radhwi, za a fassara kalmominsa a lokaci guda, ana yin shi a cikin harsuna hudu na duniya.

Ya kara da cewa: Za a tura masu ziyara da ba na Iran ba ne zuwa mashigar Darul Rahmah da Ghadir domin sauraron jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sannan kuma za su saurari jawabin shugaban a daidai lokacin da sauran mazu ziyara Iraniyawa su ma suke sauare.

Hojjat-ul-Islam Zulfiqari ya bayyana cewa: Fassarar lokaci guda zuwa harsunan Ingilishi da Larabci da Azeri da Urdu karkashin taken "Daukakar Ziyara" masana sashen fassara za su yi.

ترجمه همزمان سخنان رهبر معظم انقلاب در دو رواق حرم مطهر رضوی به چهارزبان

4128733

 

captcha