IQNA

A safiyar yau;

Ziyarar farko da jagoran juyin juya halin Musulunci ya kai a baje kolin littafi

15:36 - May 14, 2023
Lambar Labari: 3489133
A safiyar yau Lahadi 14 ga watan Mayu ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ziyarci wurin baje kolin littafai na kasa da kasa karo na 34 a birnin Tehran a masallacin Imam Khumaini.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IKNA cewa, Ayatullah Khamenei jagoran juyin juya halin Musulunci a yau Lahadi 14 ga watan Mayu a cikin sa'o'in farko na rana ta 5 na bikin baje kolin littafai na kasa da kasa karo na 34 a birnin Tehran ya ziyarci hubbaren Imam Khumaini (RA).

A yayin wannan ziyara da ta samu halartar ministan al'adu da shiryarwar addinin musulunci, Ayatullah Khamenei ya tattauna da mawallafin ya kuma yi musu karin haske.

Ziyarar karshe da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kai wurin baje kolin littafai na birnin Tehran, kafin ziyarar tasa a safiyar yau, tana da alaka da ziyarar da ya kai wajen baje kolin littafai na kasa da kasa karo na 32 a nan Tehran a ranar 9 ga watan Mayun 2018.

A cikin 2020 da 2021, saboda annobar Corona, ba a gudanar da bikin baje kolin littafai na Tehran ba tare da halartar mutane kai tsaye ba, sai dai ta hanyar yanar gizo.

 

4140721

 

Abubuwan Da Ya Shafa: jagora
captcha