Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne uwargidan shugaban kasar Amurka Jill Biden, a ziyararta a kasar Masar, ta ziyarci Masallacin Azhar.
Daya daga cikin tsare-tsaren da uwargidan shugaban kasar Amurka Joe Biden ta yi a ziyarar da ta kai kasar Masar shi ne ziyartar masallacin Al-Azhar, kuma dangane da haka ta bayyana a harabar manyan masallatai da suka fi shahara da muhimmanci na kasashen musulmi.
A cewar rahoton, Jill Biden ta mutunta al'adun Musulunci sosai a lokacin da ta shiga Masallacin Al-Azhar, ta sanya lullubi a kai sannan ta sa doguwar riga shudiyya sannan ta cire takalmanta sannan ta tafi tare da abokan aikinta suka ziyarci masallacin.
A lokacin da matar Biden ta kai ziyarar gani da ido na dadadden abubuwan tarihi, dandali, dakunan ruwa da kuma ma'adanai na masallacin Al-Azhar, wanda aka gina tun a shekara ta 1083 miladiyya, matar Biden ta saurari bayanin shugaban jami'ar dangane da tarihin masallacin.
Bayan kammala tattakin da ta yi a Masar, uwargidan shugaban kasar Amurka ta raba hotunan ziyarar da ta kai masallacin Al-Azhar a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ta kuma mika godiyarta ga jami'an jami'ar Azhar da suka karbe su.