Najaf (IQNA) Haramin Imam Ali (AS) da ke Najaf Ashraf ya karbi bakuncin dimbin masu ziyara da suka taho daga larduna daban-daban na kasar Iraki da wasu kasashe daban-daban zuwa wannan wuri mai alfarma da ke kusa da hubbaren Amirul Muminin (AS) a Eid Ghadir Khum.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, masu ziyara daga wasu kasashe daban-daban na duniya sun isa birnin Najaf Ashraf da ke kudancin kasar Iraki a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan Idin Ghadir kuma suna halartar hubbaren Imam Ali (AS).
An kawata dakin hubbaren limamin ahlul bait na farko da mashigar cikinsa da koren tutoci da sunan Imam Ali (a.s.) sannan an kawata hanyar haraminsa da furanni.
Ahmad al-Ftalavi, kakakin karamar hukumar a lardin Najaf Ashraf a cikin wata sanarwa da ya fitar, yayin da yake ishara da wuri na musamman na Idin Ghadir a cikin zukatan musulmi ya ce: Najaf Ashraf na maraba da miliyoyin maziyarta da suka zo wannan lardin. domin ziyartar haramin Imam Ali (a.s) da sauran wurare masu albarka.









