Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, wakilin kungiyar hadin kan musulmi a majalisar dinkin duniya ya fitar da sanarwar yin Allah wadai da wulakanci da kona kur’ani mai tsarki da ake yi a kasar Denmark tare da neman mahukuntan wannan kasa da su kiyaye hakkinsu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
A cikin wannan bayani da aka buga a shafin Twitter na wannan kungiya, an bayyana cewa: Muna yin Allah wadai da wulakanta kur’ani mai tsarki a kasar Denmark a kwanakin baya.
A cikin wannan bayani yana nanata cewa: Ci gaba da kare wadannan ayyuka na adawa da Musulunci da kuma rashin hana su bisa hujjar 'yancin fadin albarkacin baki, yana kara rura wutar rashin adalci a wannan fanni.
Wannan kungiya ta bukaci Denmark da ta cika nauyin da ya rataya a wuyanta bisa dokokin kasa da kasa da kuma aiwatar da kudurin kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya kan kyamar addini.
Sanarwar ta ce: Wadanda ba su daga murya ba, duk da bayyanannun umarnin hukumar kare hakkin bil'adama, za su yi saurin rasa amincin su.
A ranar 12 ga watan Yuli ne hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva ta yi Allah wadai da keta haddin kur'ani mai tsarki a karshen watan Yunin da ya gabata a kasar Sweden, duk da rashin amincewar da kasashen yammacin duniya suka yi kan kudurin da wannan majalisar ta gabatar.
Wannan kuduri ya bukaci yin Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa kur'ani, kuma bisa wannan kuduri an bayyana irin wadannan ayyuka a matsayin kiyayya ta addini.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne wata kungiyar masu adawa da Musulunci ta kasar Denmark ta kona kur'ani mai tsarki a gaban ofishin jakadancin Iraki da ke birnin Copenhagen.