IQNA

A karkashin tsauraran matakan tsaron yahudawan sahyoniya;

Dubban Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma'a a Masallacin Al-Aqsa 

18:05 - August 18, 2023
Lambar Labari: 3489661
Quds (IQNA) A yau dubban Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa mai alfarma a cikin tsauraran matakan tsaro na sojojin gwamnatin sahyoniyawan.

Dubban Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma'a a Masallacin Al-Aqsa 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada labaran Falasdinu cewa, ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta birnin Kudus ta sanar da cewa, dubban Falasdinawa mazauna birnin Kudus, da yammacin kogin Jordan da kuma yankunan da aka mamaye sun je masallacin Al-Aqsa a ranar Juma’a 27 ga watan Agusta domin gabatar da sallar Juma’a.

  A daidai lokacin da yahudawan sahyuniya ke ci gaba da jifa da duwatsu a kofar shiga masallacin Al-Aqsa na Palasdinawa. Dubban Falasdinawa ne suka gudanar da sallar asuba a masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus.

Wannan mataki ya faru ne a cikin tsarin yakin "Fajr Azim" da kuma alamar jaddada adawa da shirin raba Masallacin Al-Aqsa.

A cikin makon nan ne Falasdinawa suka gudanar da sallar asuba a cikin wani abin koyi, a daidai lokacin da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suke daukar tsauraran matakan tsaro da kuma takura musu a masallacin Al-Aqsa.

Bayan sun idar da sallar asuba, Falasdinawa masu ibada sun tattauna sirri da bukata tare da Ubangijin talikai, sannan suka ci karin kumallo a kungiyance.

 

 

 

4163309

 

 

captcha