A cewar majiyoyin labaran Falasdinu, Hazem Ismail Haniyeh daya daga cikin 'ya'yan Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas ne aka kashe a hare-haren da mayakan yahudawan sahyoniya suka kai a zirin Gaza.
Majiyoyin Falasdinawa sun bayyana cewa Hazem yana da shekaru 22 kuma dalibi ne.
A baya-bayan nan ne majiyoyin Falasdinawa suka bayar da rahoton shahadar wasu mutane 14 na iyalan Haniyeh da suka hada da Khaled Ismail Haniyeh.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya habarta cewa, Ayman Nofal daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Hamas shi ma ya yi shahada a zirin Gaza a wani harin da sojojin Isra'ila suka kai musu Noufel yana daya daga cikin mambobin majalisar koli ta soja na bataliya ta Ezzeddin al-Qassam.
4199060