IQNA

Sakamakon wani rahoto ya nuna;

Musulman Faransa na tunanin barin kasar

15:25 - May 19, 2024
Lambar Labari: 3491176
IQNA: Wani rahoto ya nuna cewa musulmin da ke zaune a kasar Faransa na tunanin barin kasar saboda yadda ake mu'amala da su.

Wani bincike da aka buga a watan da ya gabata ya nuna cewa Musulman Faransa, wadanda ke da kwarewa a  bangarori daban-daban , na neman wani sabon wurin zama a birane irin su London, New York, Montreal da Dubai domin barin Faransa.

Sakamakon binciken ya nuna cewa,  daga cikin mutane sama da dubu da suka amsa tambayoyin, kashi 71% sun ambaci wanzuwar wariya da ake nuna musu a kasar .

Adam na daya daga cikin musulmin Afrika da ke kasar Faransa wanda ya ce: Ko da yake zai yi hasarar ’yan uwa da abokan arziki ta hanyar barin Faransa, amma ya yi niyyar barin Faransa saboda kyamar addinin Islama da wariyar launin fata da yake fuskanta.

Wani ma'aikacin banki mai shekaru 30 dan asalin kasar Aljeriya, wanda ke shirin barin Faransa a watan Yuni, ya ce dangane da haka: "Yanayin Faransa ya kara tabarbarewa matuka." Ana kai mana hari ne saboda mu musulmi ne.

Ya ambaci wasu kafafen yada labarai da ’yan jarida musamman wadanda ke daukar duk musulmi a matsayin masu tsattsauran ra’ayi ko masu tayar da hankali.

 

4216580

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmi kyamar Islama kyama wariya launin fata
captcha