Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ranar 21 ga watan Agustan shekarar 2016, a yayin taro karo na biyu na majalisar manufofin hukumar kula da harkokin kur’ani ta kasa da kasa reshen Azabaijan ta gabashin kasar Iran, wanda aka gudanar a gaban mataimakin shugaban kamfanin dillancin labarai na IQNA da mambobin wannan majalisar. An baiwa babban limamin Juma’a na Tabriz Ayatullah Sayyid Muhammad Ali katin shaidar zama mamba na bangirma na Iqna .
Bayan karbar wannan kati sai wannan shahid mai daraja ya ce: Ni ma na karbi wannan kati da girmamawa, kuma na dauki kaina a matsayin ma'aikaci kuma mai hidima ga kur'ani.