IQNA

Mai rike da mabudin Dakin Kaaba na 77 tun bayan Fatahu Makka ya rasu

16:26 - June 23, 2024
Lambar Labari: 3491391
IQNA - Hukumar Kula da Masallatan Harami guda biyu ta sanar da rasuwar Saleh al-Shaibi, mutum na saba'in da bakwai da ke rike da mabudin Ka'aba tun bayan cin birnin Makkah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al Jazeera Mubasher cewa, babban jami’in kula da harkokin masallatan Harami guda biyu (Masallacin Harami da Masjidul Nabi) ya sanar da rasuwar Saleh bin Zain al-Abidin al-Shaibi babban mai rike da madafun ka'aba.

Wannan sashen ya sanar da buga wata sanarwa cewa, Saleh Al-Shaibi, mai rike da mabudin Ka'aba, ya rasu ne a yammacin ranar Juma'a 21 ga watan Yuni, kuma a ranar Asabar din da ta gabata, bayan sallar asuba a masallacin Harami, an yi sallar jana'izarsa,  kuma an bizne gawarsa a makabartar Al-Mu’ala a karshen lokacin aikin Hajjin bana.

Har ila yau masallacin al-Ahram da masallacin annabi sun fitar da sanarwa inda suka nuna alhininsu kan rasuwar babban mai kula da dakin Ka'aba.

A cewar jaridar Sabq ta kasar Saudiyya, an haifi Saleh bin Zain al-Abdin al-Shaibi bawa kuma mai rike da Ka'aba mai alfarma a shekara ta 1945 a cikin dangin da ke rike da ka'aba tun zamanin Annabi Muhammad (SAW).

Wannan jarida ta yi nuni da cewa Saleh al-Shaibi jikan “Shaiba bin Uthman bin Abi Talha ne”.

 Saleh al-Shaibi shi ne mai kula da mabudin ka'aba na saba'in da bakwai tun bayan fatahu Makkah a zamanin Manzon Allah (SAW) kuma shi ne mabudi na dari da tara tun zamanin Qusay bin Kalab, babban kakan Annabi (SAW).

Saleh al-Shaibi ya taso ne a Makka ya ci gaba da karatunsa har ya samu digirin digirgir a fannin ilimin addinin Musulunci.

Ya yi aiki a matsayin malamin jami'a kuma ya rubuta littafai da dama kan batutuwan addini da na tarihi.

Rike mabudin dakin Ka'aba matsayi ne ne mafi dadewa da daraja a Masallacin Harami da Makkah. A shekara ta 1435 bayan hijirar kawunsa Saleh al-Shaibi (Abdul Qadir Taha al-Shaibi) an dora masa wannan nauyi kuma ya dauki nauyin rike makullan dakin Kaabah.

 

4222822

 

 

 

 

captcha