IQNA - Waki’ar Ghadir dai na daga cikin manya-manyan al’amura a tarihin Musulunci, kuma masallacin Ghadir da ke da nisan kilomita biyar daga yankin Juhfa (a kan hanyar Makka zuwa Madina) shi ma alama ce ta wannan gagarumin lamari a duniyar Musulunci , ko da yake a yau wannan kasa ta zama babu kowa a cikinta, kuma an yi kokarin kawar da ita daga zukatan jam’a, amma yankin Ghadir Khum ya shaida daya daga cikin manya-manyan abubuwan da suka faru a tarihin Musulunci a lokacin Manzon Allah (saww) wanda ba za a taba gogewa daga tarihin muslunci ba.