Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Arabi ta 21 cewa, Palastinawa da dama ne suka yi shahada, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka sakamakon harin bam din da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka kai a wani dakin addu’o’i a lokacin sallar azahar a sansanin al-Shati da ke yammacin birnin Gaza.
A cewar shaidun gani da ido, jama'a da dama ne ke sallar azahar a sabon dakin sallah da ke kusa da masallacin Al-Abeez da aka lalata a yammacin sansanin Al-Shati, inda suka yi mamakin tashin bama-bamai.
Wannan harin bam ya yi sanadin shahada da raunata da dama daga cikinsu.
Shaidu sun yi nuni da cewa, an yanke akasarin shahidan gunduwa-gunduwa sakamakon tsananin ruwan bama-bamai, shaidun sun jaddada cewa, ana ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na sansanin.
Mahmoud Bassal kakakin rundunar agajin ya bayyana cewa harin da aka kai wa wannan dakin sallah ya yi sanadiyar shahadar mutane 10 tare da raunata wasu fiye da 20 kuma yawancinsu suna cikin mawuyacin hali.
Kisan gillar da aka yi wa wannan gidan addu'a a sansanin 'yan gudun hijira na al-Shati ya faru ne jim kadan bayan mummunan kisan kiyashin da Falasdinawa da dama suka yi shahada tare da jikkata wasu fiye da 280.
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa mutane 71 ne suka yi shahada a wannan kisan kiyashi, yayin da wasu 289 suka samu raunuka, kuma wasu daga cikinsu an bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali.