IQNA

Masu ziyara kimanin miliyan 5 ne suka halarci taron zagayowar wafatin Manzon Allah (SAW) a birnin Najaf

14:51 - September 03, 2024
Lambar Labari: 3491805
IQNA – Hubbaren Imam Ali (AS) ya sanar da adadin maziyarta da suka halarci taron zagayowar ranar wafatin Manzon Allah (SAW) a birnin Najaf Ashraf na Iraki da adadinsu ya kai kimanin mutane miliyan 5.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau kimanin maziyarta miliyan 5 ne suka halarci taron zagayowar wafatin manzon Allah (s.a.w) a hubbaren Imam Ali (A.S).

Shugaban sashen yada labarai na Hubbaren Alawi  Haider Rahim ya bayyana a taron manema labarai cewa: Yawan maziyarta taron makokin wafatin manzon Allah (SAW) ya kai miliyan 5.

Ya ce: Dukkan cibiyoyi da kungiyoyi da abin ya shafa sun yi kokarin saukaka zuwan maziyarta  don ziyartar Haramin Imam Ali (AS).

Shi ma gwamnan Najaf Ashraf Youssef Makki Gnawi ya sanar da samun nasarar shirin tsaro na musamman na masu ziyara domin halartar taron tunawa ranar wafatin manzon Allah (SAW).

Har ila yau, babban kwamitin tsaron masu ziyara ya sanar da cewa adadin maziyartan a Najaf ya zarce na shekarun baya.

A daidai lokacin tunawa da ranar wafatin manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar Imam Hasan Mujtaba (AS) a daidai lokacin da haramin Imam Ali (a.s) da ke Najaf Ashraf ke karbar bakuncin maziyarta  da dama da kuma gungun tawagogin maukibi, an gudanar da taruka da jawabai da kuma ziyara.

 

4234723

 

 

 

 

captcha