Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar kiyayewa da kuma buga ayyukan Ayatullah Sayyid Ali Khamenei cewa, sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran dangane da al’amuran baya-bayan nan a kasar Labanon shi ne kamar haka.
"Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai."
Kisan mutanen da ba su da kariya a kasar Labanon ya sake bayyana irin ta'asar da karen yahudawan sahyoniyawan ya nuna ga kowa da kowa, ya kuma tabbatar da gajeren hangen nesa da wauta na jagororin gwamnatin 'yan mamaya.
Kungiyar 'yan ta'addan da ke mulkin Sahayoniyawan ba su dauki darasi darasi daga yakin da suka shafe shekara guda suna yi a Gaza ba, sannan kuma sun kasa fahimtar cewa kisan gillar da ake yi wa mata da kananan yara da fararen hula ba zai iya shafar ginin kungiyoyin gwagwarmaya ba. A yanzu suna yin irin wannan siyasar wauta a Lebanon.
Ya kamata masu laifi yahudawan sahyoniya su sani ba za su iya haifar da babbar barna ga gishikin ginin kungiyar Hizbullah a kasar Labanon ba. Duk dakarun da ke gwagwarmaya a yankin suna tare da Hizbullah kuma suna mara mata baya. Dakaru masu fafutuka ne za su fayyace makomar wannan yanki, kuma na gaba-gaba a cikinsu ita ce kungiyar Hizbullah.
Al'ummar kasar Labanon dai ba su manta da cewa a wani lokaci sojojin gwamnatin 'yan mamaya sun rika sanya takalminsu har zuwa birnin Beirut ba, kuma kungiyar Hizbullah ce ta yanke kafarsu ta kuma sanya Labanon abin kauna da alfahari.
Ko a yau, Lebanon ba za ta yi nadama a kan gwagwarmayar kare kasar daga mummunan kudirin makiya ba. Wajibi ne ga dukkan musulmi su tsaya tsayin daka tare da al'ummar Lebanon da Hizbullah da dukiyarsu da kuma taimaka mata wajen tinkarar gwamnatin yahudawa azzalumai mai akata munanan ayyuka.
Amincin Allah ya tabbata ga bayin Allah
Sayyid Ali Khamenei
28 Satumba, 2024