IQNA

Paparoma ya yi kira da a mutunta addinai a Syria

16:32 - December 12, 2024
Lambar Labari: 3492378
IQNA - A cikin wani sako, Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, ya yi kira ga dukkan addinai a Syria da su nuna mutunta juna.

A cewar al-Quds al-Arabi, Fafaroma Francis ya yi kira da a mutunta juna a tsakanin dukkanin mabiya addinai a kasar Syria, kwanaki uku bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a hannun 'yan adawa masu dauke da makamai.

A yayin jawabinsa na mako-mako a hedkwatar Vatican, ya bayyana fatan al'ummar Siriya za su zauna cikin koshin lafiya a wannan kasa, kuma addinai daban-daban za su yi aiki tare da gaskiya da mutunta juna domin samun alheri ga mutanen kasar baki daya.

Paparoma ya kuma yi kira da a samar da mafita ta siyasa domin karfafa zaman lafiya da tabbatar da hadin kai a Siriya da kaucewa rikici da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar wannan kasa.

Ya kuma bukaci 'yan adawa masu dauke da makamai da suka kwace iko da kasar, da su  bi hanyoyi na lumana da  kwanciyar hankali wajen gudanar da mulki ta yadda za a samar da hadin kan kasa.

 

4253646

 

 

captcha