IQNA

Qalibaf da Araghci sun gana da Sheikh Na'im Qaseem

12:38 - February 27, 2025
Lambar Labari: 3492814
IQNA - Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Qalibaf.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibaf a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Jami’an gwomnatin 2 sun je kasar Lebanon ne don halattan taron Jana’izar manya-manyan shahidan kungiyar kuma shuwagabannin kungiyar, Shahid Sayid Hassan Nasarallah, da kuma magajinsa Sayid Hashin Safiyyuddeen. Wadanda sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka kashe ko suka kaisu ga shahada a shekarar da ta gabata.

Labarin ya kara da cewa jakadan kasar Iran a Lebanon Mujtaba Amani ya sami halattan taron inda bangarorin suka tattauna sabbin al-amura da suke tasowa a kasar da kuma yankin kudancin Asiya da kuma al-amura da suke faruwa a duniya gaba daya.

A cikin jawabin da ya gabatar a taron jana’izar dai,  sheikh Qasim ya bayyana cewa kungiyar Hizbullah zata ci gaba a kan tafarkin Shahid Hassan Nasaralla. Sannan al-amura da dama sun sauya, don haka zasu yi aikin bisa abinda suka ga ya dace a ko wani lokaci.

 

 

4268527

 

captcha