IQNA

Kasar Saudiyya na shirin raba kur'ani fiye da miliyan daya a duniya

14:40 - February 27, 2025
Lambar Labari: 3492815
IQNA - Kasar Saudiyya na raba kwafin kur’ani miliyan daya da dubu dari biyu ga kasashe daban-daban na duniya a albarkacin watan Ramadan.

Shafin yanar gizo na news.elsob7 ya habarta cewa, sarki Salman bin Abdulaziz na kasar Saudiyya ya sanar da amincewarsa na raba kur’ani mai tsarki miliyan daya da tafsirinsa cikin harsuna 79 a cibiyoyin muslunci da al’adu da kuma ofisoshin cibiyoyin addini a cikin ofisoshin jakadancin Saudiyya da ke kasashe daban-daban na duniya.

An aiwatar da wannan kuduri ne bisa tsarin bayar da kyautar kur’ani mai tsarki na Sarkin Saudiyya (Kyautar mai kula da masallatai masu alfarma guda biyu), kuma ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci da yada farfaganda da shiryarwa ta Saudiyya ce ke kula da ita.

Za a gudanar da wannan aiki ne a watan Ramadan na wannan shekara (Ramadan 1446), kuma za a gabatar da wadannan kur’ani ga musulmi a kasashe 45 daban-daban na duniya.

Dangane da haka ne ministan harkokin muslunci na kasar Saudiyya ya bukaci hukumar da'a da buga kur'ani ta sarki Fahad da ke Madina da ta kara yawan buga kur'ani da tafsirin kalmar saukar.

 

 

4268492

 

 

captcha