IQNA - Ala Azzam makaranci Falasdinawa kuma mawakin wake-wake na addini ya yi shahada tare da dukkan iyalansa a wani da na Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Quds cewa, Ala Azzam, wani shahararren makaranci da karantarwa na Falasdinu ya yi shahada tare da iyalansa a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a gidansa da ke yankin Tel Al-Hawa a birnin Gaza.
A kasa ga bidiyon wannan shahidi Bafalasdine.