IQNA

Paparoma Ya Yi Gargadi GameDa Yiwuwar Barkewar Yakin Duniya Na Uku

18:46 - January 10, 2026
Lambar Labari: 3494477
IQNA - PaparomaLeo na 14 ya yi gargadi kan yiyuwar barkewar yakin duniya na uku bisa la'akari da siyasar da Amurka ta dauka a yanzu na yin shishigi a kan kasashe.

Jagoran mabiya addinin kirista mabiya darikar Katolika na duniya PaparomaLeo na 14 ya yi gargadi kan yiyuwar barkewar yakin duniya na uku bisa la'akari da siyasar da Amurka ta dauka a yanzu na yin shishigi a kan kasashe musamman bayan katsalandan data yi a cikin lamarin Venezuela da kuma sace shugaban kasar.

Paparoma ya bayyana takaicinsa matuka dangane da yaddaAmurka take neman mayar da kanta wata yar sanda ta duniya taredacin karenta babau babbaka a kan kasashe masu 'yanci.

Ya ce irin wadannan ayyuka za su iya jefa duniya cikin wanimummunan hadari da ka iya kaiwa ga yakin duniya wanda kuma hakan ba zai yi kowa dadi ba harda ita kanta Amurka.

Dangane da takaita 'yancin fadar baki a nahiyar Turai,Paparoma ya bayyana cewa,baya jin dadin yadda ake tauye hakkokin mutane wajen bayyana ra'ayinsu ko fadar albarkacin baki.

 

4327910

captcha