
Babban mufti na kasar Rasha Nafiullah Asirov ya bayyana cewa, Sulaiman Muhammadov malamin addini a Raasha ya kaddamar da sabuwar tarjamar kur'ani mai tsarkia cikin harshen rashanci, wanda zai amfanar da al'umma.
Ya ce wannan babban aiki ne mai matukar muhimmanci ga al'ummar Rasha ba kawai ga musulmin kasar ba, har ma da wadanda suke son sanin abin da kur'ani yake kunshi da shi.
Ya kara dacewa, za a ci gaba dabuga wannan tarjama domin rabawaga al'umma da kuma fatan hakan ya zama mai amfani wajen isar da sakon addinin musulunci.
Baya ga haka kuma ya yi ishara da cewa, wannan ba shi ne karon farko da aka tarjama kur'ani a cikin harshen rashanci ba, amma kuma wace tarjama tana dawasu abubuwa na musamman data kebantu dasu.
4328987