Bangaren kur'ani: Idin Norouz rana ce ta fara haduwar dangi da junansu bisa al'ada da mahangar Musulunci ta yi na'am da ita a cikin kur'ani, bisa hujjar kara karfafa dankon zumunci tsakanin iyalai baki daya.
A wata zantawa da ta hada wani masani kan ilmomin kur'ani da kamfanin dillancin labaran Ikna (Ali Reza Mohammadi) ya bayyana cewa; Idin Norouz rana ce ta fara haduwar dangi da junansu bisa al'ada da mahangar Musulunci ta yi na'am da ita a cikin kur'ani, bisa hujjar kara karfafa dankon zumunci tsakanin iyalai baki daya, ya ci gaba da cewa yanayin Bahar yanayi ne na farkon shekara, kuma dama ce ta sada zumunci tsakanin dangi da 'yan gami da bokan arziki, inda suke gudanar da bukukuwa na jin dadi da annashawa sakamakon ganin junansu. Ya ce a cikin kur'ani Allah madaukakin sarki ya karfafa batun sada zumunta tsakanin dangi a cikin ayoyi da dama, wanda kuma damar da mutane suke yi amfani da ita a lokutan idin Norouz zai iya zama dam ace ta yin aiki da umurnin ubangiji.
379182