Bangaren adabi: Littafin ilmomin kur'ani wanda musatafa Asrar ya rubuta mdaba'ntar Sabz Arang ta yada shi a cikin lokacin hunturun shekarar da ta gabata ta 87 hijira shamsiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; littafin ilmomin kur'ani wanda musatafa Asrar ya rubuta mdaba'ntar Sabz Arang ta yada shi a cikin lokacin hunturun shekarar da ta gabata ta 87 hijira shamsiyya.
Littafin wanda aka rubuta shi domin gano ilimomin da ke cikin kur'ani, ya mayar da hnkali ne kan abubuwan da aka fi gudanar da bincike kansu, wadanda daga bisani dan adan ke gano sirrin ilmomin da ke tattare da su, wanda kuma tuni kur'ani ya kawo su, duk da cewa wasu lokuta marubucin yak an takaitu da bayanai kan ma'anonin zahiri na ayoyi dangane da ilmomin, amma wasu lokuta yak an nisanta cikin bincike domin wrware wasu lamurran bisa bayanai na malamai, domin kuwa ba dukkanin ayoyin kur'ani ne suka zo da bayanai a rarrabe, wasu ayoyin na bukatar komawa zuwa ga dalilan safkarsu da kuma bayanan masu ilimin tafsi kansu.
380781