IQNA

An Kawo Karshen Baje Kolin Kur'ani A Birtaniya

Bangaren al'adu da fasaha: An kammala baje kolin fasahar musulunci da rubutun hannu na kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Peterporo na kasar Birtaniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an kawo karshen baje kolin fasahar musulunci da rubutun hannu na kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Peterporo na kasar Birtaniya, wanda aka fara gudanarwa tun makonni uku da suka gabata domin murnar tunawa da zagayowar ranakun maulidin manzon Allah (SAW) da kuma Imam Ja'afar Sadiq (AS) da kuma raya makon hadin kai tsakanin al'ummar musulmi.
A lokacin bude taron baje kolin manyan malamai gami dam asana sun halarci wurin daga birane daban-daban na kasar Birtaniya, inda shugaban majalisar musulmin birnin Peterporo (mohammad Qasim) ya gabatar da jawabi a gaban daruruwan masana musulmi da suka hada da mabiya mazhabar shi'a da kuma 'yan sunna gami da mabiya addinin kiristanci.


381077