Bangaren al'adu da fasaha: Bisa manufa ta karfafa harkokin addini an raba littafan addini daban-daban sama da 2000 a garin Kohdasht da ke cikin lardin Lorestan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya zanta tare da shugaban cibiyar yada addini na yankin Lorestan Hojjatol Islam (Geravand) inda ya bayyana cewa; a kokarin da cibiyar ke na karfafa harkokin addini an raba littafan addini daban-daban sama da 2000 a garin Kohdasht da ke cikin lardin Lorestan. Ya ci gaba da cewa babbar manufar yin hakan ita ce wadata yankunan da littafai na nazari, domin masu sha'awar karatu su samu littafan addini da za su taimaka musu wajen sanin addini yadda ya kamata, kamar yadda hakan zai taimaka ma masu isar da sako da masu wa'azi wajen samun littfan da za su yi amfani da su a masallatai.
381404