IQNA

An Kafa Kwamitin Kare Masallacin Qods Ta Hanyar Internet

Bangaren kasa da kasa: Shafin internet na islam online ya bude wani bangare da ya kira kwamitin kare masallacin Qods, domin bayar da kariya tare da wayar kan al'ummomin duniya kan barazanar da yahudawan sahyuniya ke yi kan wurare masu tsarki da ke Qods, wadanda dukkanin addinai da aka safkar daga sama.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Islam Online cewa; wannan shafi ya bude wani bangare da ya kira kwamitin kare masallacin Qods, domin bayar da kariya tare da wayar kan al'ummomin duniya kan barazanar da yahudawan sahyuniya ke yi kan wurare masu tsarki da ke Qods, wadanda dukkanin addinai da aka safkar daga sama.Bayanin ya ci gaba da cewa ta hanyar wannan kwamiti za a samu masaniya tare da tattara bayanai da suka shafi halin masallacin Qods mai alfarma yake ciki, tare da sanin yanayin da mutanen birnin Qods muslmi palastinawa suke ciki, An kafa wannan kwamitin ne a daidai lokacin yahudawan sahyuniya suke tunawa da mamaye palastinu da suka a cikin shekara ta 1948.


402321