Bangaren al'adu da fasaha; Babban daraktan cibiyar mahdawiyya mahmud Babbayi ya bayyana cewa jahilci da rashin masaniya na daya daga cikin abin da ke cutar da msulmi,
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai da hulda da jama'a na cibiyar mahdawiyya cewa; Babban daraktan cibiyar mahdawiyya mahmud Babbayi ya bayyana cewa jahilci da rashin masaniya na daya daga cikin abin da ke cutar da msulmi, musamman ma bangaren mahdawiyya da mazhabar shi'anci ke shan wahala wajen daidaita tunaninsu. Daga cikin muhimman abubuwan da taron ke yin dubin a kansu har da daukar matakai na mayar da martani a ilmance dangane da yadda wasu masana a jami'oin kasashen turai suke kokarin gurbata manufar addinin musulunci a cikin nahiyar turai, wanda hakan na bukatar masana musulmi musamman ma dai malaman jami'oi su mayar da hankali kansa domin kare addinin musulunci daga zagon kasa.445315