IQNA

Taro Mai Taken Yaki Da Ta’addanci A Cikin Kur’ani A Masar

23:31 - October 30, 2019
Lambar Labari: 3484206
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da zaman taro mai taken yai da ta’addanci a cikin kur’ani a birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya an fara gudanar da zaman taro mai taken yai da ta’addanci a cikin kur’ani a birnin Alkahira na kasar Masar.

Taron yana samun halartar malamai da masana da suka hada da Sa’aduddin Hilali, shugaban bangaren fikihu an Azhar, Khalid Ukasha, da kuma Abdulmuhsin Muhammad Abdulradi da sauransu.

Babban abin da taron yake yin dubi a kansa shi ne, yadda alkur’ani mai tsarki ya zama a sahun gaba wajen yaki da duk wani nauin ta’addanci, da kare hakkin dan adama, da yada zaman lafiya da adalci a tsakanin al’ummomi.

Haka nan kuma masana da malamai suna gabatar da kasidunsu a kan taron kan yadda dukkanin masu bincike za su iya gano ayoyi da suke yin magana kan zaman lafiya a cikin kur’ani da kuma yin watsi da duk wani salon a ta’addanci da rashin imani a cikin zamantakewar al’umma.

3853515

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha