IQNA

Halartan kasashe 66 a gasar kur'ani mai tsarki ta "Port Said" a kasar Masar

23:06 - January 31, 2022
Lambar Labari: 3486889
Tehran (IQNA) A wata mai zuwa ne za a gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa "Port Said" a kasar Masar tare da halartar kasashe 66.

A watan gobe ne za a gudanar da gasar haddar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a lardin Port Said na kasar Masar a zagaye na biyar tare da halartar wakilai daga kasashe 66.

Adel Masilahi, mai ba da shawara kan yada labarai na lardin Port Said kuma mai kula da gasar kur’ani ta kasa da kasa karo na 5 na Port Said, ya sanar da cikkaken bayanin gasar.

"An fara gasar ne a shekarar 2003 a matakin larduna uku na Suez, sannan ra'ayin ya yadu kuma aka gudanar da ita a matakin lardunan Masar," in ji shi.

Jami’in na Masar ya kira gasar da mai matukar muhimmanci ga harkokin yawon bude ido da al’adu da addini a Masar, musamman a birnin Port Said, ya kuma ce an shirya tawagogin kasashen waje da ke halartar gasar za su ziyarci wuraren yawon bude ido na tarihi a birnin Port Said.

 

4032661

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: addini muhimmanci matakin larduna
captcha