IQNA

Maraba da shigowar watan Azumin Ramadan a Kasashen Musulmi

TEHRAN (IQNA) – Ranar Alhamis aka fara ganin watan Ramadan mai albarka a galibin kasashen musulmi.

Musulmai na maraba da watan mai alfarma tare da gudanar da ayyuka daban-daban kamar kakkabe  kura da tsaftace masallatai da wurare masu tsarki, yin ado da haskaka tituna, sayen sabbin tufafi, dafa abinci na musamman da kayan zaki, gudanar da shirye-shiryen karatun  Alkur'ani, halartar sallolin jam'i da bayar da abinci ga musulmi a wurin taruka a lokacin buda baki.